Har gobe talakawa na kaunar APC, zamu ci zabe a 2023 kamar yadda mukayi a 2015 da 2019 – inji Buhari
Daga Muryoyi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ko shakka baya yi jam’iyyar APC ce za tayi nasara a zaben shugaban kasa a 2023 kamar yadda tayi a 2015 da 2019.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacinda ya yi wata ganawa da wasu jiga-jigan jam’iyyar domin lalubo dan takarar da yafi cancanta APC ta tsaida a babban zabe mai zuwa wanda taron ya gudana a daren jiya Lahadi a Abuja.
- Advertisement -
Muryoyi ta ruwaito Buhari na cewa zuwa yanzu ya tuntubi kungiyar Gwamnonin APC, da su kansu yan takarar da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar kuma ganawar tana haifar da d’a mai ido.
Shugaba Buhari yayi amanna har gobe talakawa suna kaunar jam’iyyar APC kuma ita zata yi nasara da gagarumin rinjaye a zaben shugaban kasa da na Majalisun tarayya da Gwamnoni a 2023