In sha Allahu Tinubu zai kayar da Atiku a zaben 2023 cikin sauki –inji El-Rufai 

In sha Allahu Tinubu zai kayar da Atiku a zaben 2023 cikin sauki –inji El-Rufai

 

Daga Muryoyi

 

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai yace kayar da Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa abu ne mai sauki domin sun san shi sun san tsarinsa da karfin sa.

 

A hirarsa da Chennels TV Gwamnan ya ce Tinubu ya dama Atiku ya shanye a dabarar iya cin zabe, domin shi tsohon dan siyasa ne mai jajircewa wanda ya iya lale wasansa.

 

- Advertisement -

A cewar Gwamnan duk da dai ba zasu je suyi bacci ba amma dai sun san Kwankwaso zai raba kan kuri’un APC a jihar Kano da Jigawa da kila wani sashi na Katsina to hakanan Peter Obi dan takarar Labour Party zai raba kan kuri’un PDP a Kudu.

 

“Kanina na Omosure kuwa na jam’iyyar AAC nasan watakila ya samu kuri’u dubu 30. Amma tabbas in sha Allahu APC ce za tayi nasara a zaben 2023 sai ma dai Tinubu ya dauko mataimakinsa ku sha mamaki”

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: