Jami’an tsaro Uku sun sume yau a filin faretin ranar dimokuradiyya

Jami’an tsaro Uku sun sume yau a filin faretin ranar dimokuradiyya

 

Daga Muryoyi

 

Rahotanni na nuna cewa Jami’an tsaro Uku sun fadi a sume ana tsaka da gudanar da faretin bikin ranar dimokuradiyya yau Litinin a Abuja

 

Majiyar Muryoyi ta ruwaito gamayyar Sojojin kasa da na sama da na ruwa da kuma yan sanda ne da sauran su suka gudanar da faretin wanda yayi daidai da faretin ban kwana ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda wa’adin mulkinsa zai kare kafin bikin badi.

 

- Advertisement -

Faretin wani atisaye ne na shekara-shekara da ake gudanarwa domin girmama dawowar al’ummar kasar kan turbar mulkin farar hula da kuma tunawa da dadin romon dimokradiyyar Najeriya.

 

Bayanai sun ce nan da nan rukunin kula da kiwon lafiya suka kai masu dauki aka kwashe su akayi masu magani suka farfado. Ance sun jima a tsakiyar filin wanda rana ta dakesu sosai a yayin faretin

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: