Kirista daga Arewa maso Gabas nake son dauka mataimaki ba wanda zai mani karfa-karfa –inji Tinubu 

Kirista daga Arewa maso Gabas nake son dauka mataimaki ba wanda zai mani karfa-karfa –inji Tinubu

 

Tinubu ya yi Allah-wadai da jita-jita kan tikitin musulmi da musulmi

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yadawa na cewa yana da niyyar zabar dan uwansa musulmi a matsayin abokin takararsa.

 

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida yayin taron gangamin jam’iyyar APC da aka gudanar jiya a Ekiti gabanin zaben gwamna da za a yi a jihar.

 

 

- Advertisement -

Sai dai ya nisanta kansa daga wannan jita-jita, yana mai jaddada cewa masu yada wannan magana makiyansa ne da basa son yaci zabe.

 

 

Muryoyi ta ruwaito da dan jarida ya tambaye shi kan zabin mataimakin shugaban kasa, Tinubu ya ci gaba da cewa Mataimakinsa zai fito ne daga yankin Arewa maso Gabas kuma musamman Kirista, duk da cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa kan wanda za a yanke shawarar dauka.

 

 

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa babu wani mutum ko wata kungiya ko cibiya da zai iya yi masa karfa-karfa ya dora masa mataimakin shugaban kasa. A cewarsa shi zai zabi mataimakin shugaban kasa da kan sa wanda yan Najeriya ke so.

 

 

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: