Kungiyar CAN tace ba zata yarda APC ta tsaida Muslim da Muslim takara ba a zaben 2023
Daga Muryoyi
Kungiyar Kiristoci ta kasa CAN ta gargadi jam’iyyun siyasa a Najeriya da kada su kuskura su zabi Musulmi da Musulmi a matsayin yan takaran Shugaban kasa da mataimakinsa a zaben 2023.
A sanarwar da sakataren kungiyar na kasa, Joseph Bade Daramola, ya fitar a yau Juma’a CAN ta ce “Ba za ta taba yarda Tinubu ko Atiku su zabi Musulmi a matsayin mataimakansu ba”
- Advertisement -
Majiyar Muryoyi ta ruwaito kungiyar tace ko a yanzu da ake shinkafa da wake suna shan wahala ina ga mulki ya koma hannun Musulmai gaba daya.
Ta ce a yanzu ba 1993 bane lokacinda ake hada Musulmi da Musulmi amma CAN tace a yanzu kan mage ya waye hakan ba zata sabu ba.
Wannan dai na zuwa ne a lokacinda Hukumar zabe ta kasa INEC ta baiwa Tinubu da Atiku da su Kwankwaso wa’adin mako guda su mika sunayen abokan tafiyarsu