Mahaifin Aysha ya rasu lauyar da ta kare masoya manzon Allah a rikicin Sokoto
INNA LILLAHI WA INA ILAIHI RAJIUN
Allah yayi wa mahaifin Barrista Aysha Alhaji Ahmad Mohammad rasuwa a yau Juma’a, 10 ga watan Yuni, 2022
Muryoyi ta ruwaito margayin ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a asibiti Shika dake Zaria.
Ana sa rai za ayi Jana’izarsa yau da misalin karfe 5:30 na yamma In Sha Allah a gidansa dake Gangare Tudun Wada Zaria jihar Kaduna.
- Advertisement -
Margayin ya rasu ya bar iyali da ya’ya cikinsu har da Barrista Aysha Ahmad fitacciyar lauya mai kare talakawa kana sakatariya a ma’aikatar tara kudaden haraji ta jihar Kaduna.
Barrista Aysha itace wacce ta yi rubutun kan “Defense of Provocation” domin kariya ga masoya manzon Allah S.A.W a lokacinda abubuwa suka kacame a rikicin Sokoto