NASA tace ta hangi wani abu kamar wutar Jahannama amma zata tsananta bincike

NASA tace ta hangi wani abu kamar wutar Jahannama amma zata tsananta bincike akai

Daga Muryoyi

Hukumar kula da sararin samaniya wato NASA ta sanar da shirinta na tsananta bincike kan wata duniya wacce ke ci da wuta mai tsananin zafi. Anyi wa duniyar lakani da “55 Cancri e”

Binciken da akayi zuwa yanzu ya nuna cewa tsananin narkon azabar zafin dake cikin wannan duniya ta wuta zai iya narkar da duwatsun duniya ya hurar dasu kamar toka sannan zai iya tafarfasa duka ruwan duniya a cikin dan kankanin lokaci.

- Advertisement -

Sun ce irin azabar radadi da zafin wutar wacce a yanzu tazararta da duniyar rana yafi tafiyar shekara dubu 50, azabar tayi kama da wutar Jahannama da aka fadi a cikin littafi mai tsarki

Muryoyi ta ruwaito NASA ta ce duniyar 55 Cancri e tana da tsananin zafi wanda idan da zata kusanci duniyar mu ko kadan ne to da anyi ruwan wuta sannan komi zai narke. Tsabar azaba shekara zata iya komawa kamar sati, sati zai koma kamar yini.

Babu wani abu mai kama da ita a wannan duniyar da sararin samaniya a cikin tsarin hasken rana, in ji NASA.

Abunda yafi dagawa masana hankali shine duk wannan narkon azabar da aka lissafa na tsananin zafi “a bayan duniyar ce kawai ba aga asalin gaban duniyar ba ta inda asalin zafin yake”

Muryoyi ta ruwaito NASA ta ce wani abun alajabi na faruwa a cikin ita wannan duniyar ta 55 Cancri e, mai kama da duniyar rana wanda zasu so sanin menene shi yasa suka kirkiri wata na’ura ta hange wato James Webb da take son tayi amfani dashi ta gano ko yaya duniyar take sannan me ke konewa a cikinta.

Kullum duniyar tana cikin ci da wuta don haka masana ke son tsananta bincike akai

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: