Rashin tsaro: Kungiyar CAN ta nemi Gwamnati ta bari kowa ya mallaki bindiga

Rashin tsaro: Kungiyar CAN ta nemi Gwamnati ta bari kowa ya mallaki bindiga

Daga Muryoyi

Kungiyar Kiristoci ta kasa CAN ta bukaci Gwamnatin tarayya ta kafa dokar da za ta baiwa mutane damar daukar makamai a Najeriya.

Wannan bayani na kunshe ne a martanin da kungiyar CAN reshen jihar Ondo tayi kan harin da wasu yan bindiga suka kai a cocin katolika na St. Francis Catholic Church, dake Owo a jihar Ondo makon da ya gabata wanda yayi sanadiyyar mutuwar Gomman mutane.

- Advertisement -

Majiyar Muryoyi Sunday PUNCH ta ruwaito a takardar bayan taro da kungiyar ta fitar dauke da sa hannun shugabanta, Rev. Fr. Anselm Ologunwa, da Sakatare, Very Evang. Amos Olomofe, da kuma daraktan yada bayanai, Mr Daisi Ajayi ta roki a halasta rike makami don kare kai.

CAN ta ce , “Kundin tsarin mulkin Najeriya na yanzu wanda ya haramta amfani da bindigogi, kamata ya yi a sake duba shi ayi gyare-gyare a ciki, domin baiwa daidaikun mutane damar kare kansu, duba da irin halin rashin tsaro da kasar ke ciki.”

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: