Shugaban APC na kasa ya boye kansa tun jiya “Deliget sun nemi sai yayi murabus”

Shugaban APC na kasa ya boye kansa tun jiya “Deliget sun nemi sai yayi murabus”

Daga Muryoyi

Rahotannin na nuna shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu yayi batan dabo tun jiya bayan da aka ruwaito ya gayawa kwamitin gudanarwar jamiyyar cewa Buhari ya turo shi ya gaya masu Ahmed Lawan ne dan takararsa na maslaha.

Sai dai shugaban kasar ya nesanta kanshi daga wannan ikirari na Adamu, hakanan yan kwamitin gudanarwar jam’iyyar da Gwamnonin APC duk sunyi fatali da zabin Sanatan.

- Advertisement -

Daga bisani aka ruwaito yadda Adamu ya fatattaki yan jarida daga harabar sakatariyar APC bayan da bayanin nasa ya yamutsa hazo.

Muryoyi ta ruwaito Gwamnoni da yan kwamitin gudanarwar jam’iyyar da wakikan jam’iyya (Deliget) suna neman Abdulahi Adamu amma sun gaza gano shi.

Tijjani Ramalan shugaban kafafen yada labarai na Liberty TV da Radio ya ce wayoyinsa a kashe sannan yaki halartar jerin tarurrukan da akayi a daren jiya.

Tuni dai Deligate da wasu wakilan jam’iyya suka nemi sai Abdullahi Adamu yayi murabus daga mukaminsa na shugabancin jam’iyyar APC bayan abunda yayi na tsayar da Ahmed Lawan a matsyin dan takara.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: