Tinubu ya lashe zaben fidda Gwani na APC, Amaechi na Biyu, Osinbajo na Uku

Tinubu ya lashe zaben fidda Gwani na APC, Amaechi na Biyu, Osinbajo na Uku

Daga Muryoyi

Jagoran APC na kasa, tsoho Gwaman jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu, ya lashe zaben fidda Gwani na jam’iyyar APC da kuri’u 1,271 bayan ya doke abokan karawarsa su 13 da suka hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, da ministan sufuri Rotimi Amaechi, da kakakin majalisa, Ahmad Lawan.

Deligat 2,300 suka yi zabe a zaben fidda Gwani da ya gudana jiya a Abuja.

- Advertisement -

A yanzu Tinubu zai kara da dan takarar PDP, Atiku Abubakar da Kwankwaso na NNPP da sauran su a zaben da za ayi a ranar 25 ga watan February 2023.

Yan takarar 14 sun samu kuri’u kamar haka Tinubu 1,271, sai Rotimi Ameachi ya zo na Biyu da kuri’u 316, sai Osinbajo ya zo na Uku da kuri’u 235, Shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan ya samu 152, Umahi 38, sai Rochas Okorocha ba ko daya wato – 0,

Sauran sune Yahaya Bello 47, Tein Jack-Rich – 0, Emeka Nwajiuba – 1, Ben Ayade – 0, Ikeobasi Mokelu -0, Ogbonnaya Onu – 1, Tunde Bakare – 0 sannan sai Sani Yerima -1.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: