Tsaro: Majalisa ta amince Ganduje ya ciyo bashin Biliyan N10 don saka CCTV a Kano 

Tsaro: Majalisa ta amince Ganduje ya ciyo bashin Biliyan N10 don saka CCTV a Kano

Daga Muryoyi

Majalisar dokokin jihar Kano, ta amincewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya karbo bashin Naira Biliyan Goma domin amfani da kudin wajen sanya na’urorin CCTV domin kyautata tsaro a jihar.

Majiyar Muryoyi ta ruwaito Gwamna Ganduje ya aikewa majalisar wasika inda kuma Shugabanta Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya karanta a zaman majalisar na ranar Laraba.

- Advertisement -

Freedom Radio ta bayar da labari cewa Gwamnan a cikin wasikar ya ce, za a sanya na’urorin ne la’akari da barazanar tsaro da jihar ke fuskanta a ƴan kwanakinnan.

“Nan take bayan tattauna batun ne tare da bada shawarwari ƴan majalisar suka amince a ciyo bashin” inji wakilin majiyar Muryoyi

 

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: