Wallahi duk ‘Yan takarar nan na shugaban kasa babu wanda ya san matsalar Arewa kamar ni ku zabe ni –Rochas ya fadawa deliget
Daga Muryoyi
Wallahi duk ‘Yan takarar nan na shugaban kasa babu wanda ya san matsalar Arewa kamar ni, saboda na jima ina rayuwa a cikin Arewa don haka ni ne kawai na cancani ku zabe ni don nine masoyin ku na gaskiya ba sai da siyasa ta zo ba
Idan nayi nasarar zama shugaban kasa nayi alkawari zan fatattaki talauci da yunwa, sanann bana neman shugabanci don na azurta kaina sai don ceto Al’ummar Kasar nan daga mawuyacin halin da ta tsinci kanta cewar Sanata Rochas Okrocha a jawabin da yayi wa deligate a daren yau a wajen zaben fidda Gwani
- Advertisement -