Wannan mutum ba karamin darasi bane garemu …Allah yasa mu gama lafiya

Wannan mutum ba karamin darasi bane garemu …Allah yasa mu gama lafiya

Daga Suleiman Ibrahim Dabo

Kwana biyu da suka gabata (ranan laraba) na ziyarci ofishin Jam’iyan APC dake kan Ali Alkilu way a Jahar Kaduna, A lokacin da naje zan shiga sai naga wannan bawan Allah yana gyaran takalmi kuma yana siyar da sabulun wanki na leda.

Da na lura da kyau sai naga a zatona ciwon shan inna ne ya kamashi ya samu nakasa

- Advertisement -

Amma wannan baisa zuciyan shi ta mutu ba sai ya kama sana’a. Sai na cire takalmi na na bashi yayi mun polish na dauki kudi mai nauyi na bashi don ya inganta sana’an shi.

Ina Kira ga masu lalura irin na shi da wanda bai kai nashi ba, da wanda ya wuce nashi dasu karfafa zukatan su. Su sani cewa Allah na son su kaman yanda yake son kowa, zai taimake su kaman yanda yake taimakon kowa.

 

Kada su dauka bara shine mafitan su, su sani zasu iya yin Sana’a kaman kowa. Wannan mutum ba karamin darasi bane garemu. Allah yasa mu gama lafiya.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: