YANZU-YANZU: An fara tantance deliget da za su kada kuri’a a zaben fitar da Gwani na APC a yau

Kai tsaye daga Babban Birnin Tarayya Abuja: An soma tantace daliget-daliget da za su kaɗa kuri’a a zaɓen fitar da gwani na neman tikitin takara a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Sama da daliget dubu biyu ne za su tantace domin zabo mutumin da zai fafata da ɗan takarar jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2023 da ke tafe.

Za a gudanar da zaɓen ne a dandalin Eagles square kuma kusan an kammala duk wasu shirye-shirye.

An tsaurara matakan tsaro, sannan an sauya fasalin wajen taron.

- Advertisement -

Mutum 23 ne suka nuna sha’awarsu ta takara a karkashin inuwar APC.

Fitattun a cikinsu akwai, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: