Thursday, March 23, 2023
HomeBatutuwaAdabiZa muyi nasara a kan 'yan ta'adda da 'yan korensu masu haddasa...

Za muyi nasara a kan ‘yan ta’adda da ‘yan korensu masu haddasa fitina -cewar Buhari a jawabinsa na ban kwana

Za muyi nasara a kan ‘yan ta’adda da ‘yan korensu masu haddasa fitina -cewar Buhari a jawabinsa na ban kwana

Daga Muryoyi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga duka ƴan Najeriya su saka waɗanda rikicin ta’addanci ya rutsa da su a cikin addu’a.

Buhari a jawabinsa na ranar dimokuradiyya wanda shine na karshe a mulkinsa ya ce kullum yana kwana yana tashi da tsananin baƙin cikin waɗanda harin ta’addanci ya rutsa dasu da wadanda aka yi garkuwa da su inda ya ce shi da duka hukumomin tsaron Najeriya suna yin bakin kokarinsu domin ganin an ceto su.

- Advertisement -

Buhari ya kuma bayyana muhimmancin ranar dimokraɗiyya inda ya jaddada muhimmancin zaɓen Yunin 1993 a tarihin Nijeriya, ya ce kada ƴan Najeriya su manta da irin gudunmawa da sadaukar da kai da gawarazan dimokraɗiyya suka bayar a 1993.

A saboda haka sai ya buƙaci jama’a da su yi koyi da kishin ƙasa irin na magabata a duk lokacin da za su zaɓi shugabanni a kowane mataki.

Ya sake tuna wa ƴan Najeriya cewa wannan ita ce ranar dimokraɗiyya ta ƙarshe da zai yi a matsayinsa na shugaban ƙasa inda ya ce yana cike da ƙudirin tabbatar da cewa an zaɓi sabon shugaban ƙasa ta hanyar zaɓen gaskiya da adalci

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma yaba da yadda aka gudanar da zaɓen fitar da gwani a duka jam’iyyun kasar inda ya ce ɗaya daga cikin abin da ya birge shi da zaɓen shi ne yadda mata da matasa a kusan duka jam’iyyun suka fito neman takara inda ya ce wannan alama ce da ke nuna dimokraɗiyya ta ƙara bunƙasa a Najeriya a cikin shekara 23 da aka shafe.

Shugaban ya bayyana cewa a shekara bakwai da gwamnatinsa ta shafe tana mulki, ta yi ƙoƙari wurin gyara dokokin zaɓe da yanayin gudanar da zaɓen domin kare ƙuri’un yan kasa.

BATUN TSARO

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna damuwarsa kan halin rashin tsaro da ƙasar ke fama dashi, yana mai cewa “abin na damun sa a kullum”.

Cikin jawabin nasa dai na a yau Lahadi, Buhari ya ce waɗanda suka rasa rayukansu, za su ci gaba da nema wa iyalansu adalci a kan miyagun sannan waɗanda suke rike a hannu kuma a yanzu, Gwamnati ba zata saurara ba har sai an sako su kuma an gurfanar da masu garkuwa da su a gaban kotu.

“Idan muka haɗa kanmu za mu yi nasara a kan ‘yan ta’adda da ‘yan korensu masu haddasa fitina.” Inji Buhari

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: