Zan marawa Tinubu baya yaci zabe don shi yafi dacewa ya mulki Najeriya –inji Buhari
Zan marawa Tinubu baya yaci zabe don shi yafi dacewa ya mulki Najeriya –inji Buhari
Daga Muryoyi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ne mutumin da ya fi dacewa ya mulki Najeriya a 2023 kasancewarsa gogge wanda yasa siyasa da Dimokuradiyya.
Buhari ya kara da cewa yana tare da Bola Tinubu kuma zai mara masa baya wajen cimma nasara a babban zaɓen da za ayi a 28 ga watan Fabairu 2023.
- Advertisement -
A cewar shugaban kasar Tinubu shi ne mutumin da zai kare sannan ya inganta tsarin dimukuradiya da aka gina kasar a kai.
Sannan sai Buhari ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar APC da su hada kai wajen ganin sun cimma nasara a zaɓen 2023.