2023: Kaji tsoron Allah, Kaji tsoron Shaidan, Kaji tsoron Dan PDP –inji El-Rufai
El-Rufai ya gargadi yan Najeriya kan zaben jam’iyyar PDP, a cewarsa Jam’iyyar PDP abun tsoro ce abun gudu ce saboda lalacinsu ga kasa
“Sunyi yunwan shekara 8 idan kuka sake suka sake karbar mulki to ba ma abunda aka tara a baitul mali ba, har abunda ka ajiye a gidanka sai sun zo sun kwashe Kaji tsoron Allah, Kaji tsoron Shaidan, Kaji tsoron Dan PDP” inji El-Rufai
Gwamnan yayi wannan Jan hankalin ne a yau Laraba a yayin da ake hirar yan Jarida ta kai tsaye tare da shi.
- Advertisement -