An garzaya da Ministan Indiya Asibiti bayan ya sha ruwan Kogin mazabarsa

An garzaya da Ministan Indiya Asibiti bayan ya sha ruwan Kogin mazabarsa

Daga Muryoyi

Ministan Indiya, mai shekaru 48, da ya sha datti daga kogin ‘tsarki’ wanda aka gurbata da najasa don nunawa mazauna yankin cewa lafiya lau ne ruwan ya kamu da rashin lafiya.

Bhagwant Mann, babban ministan Punjab ya sha ruwane da nufin nunawa mazabarsa ruwan Kogin tsaftatacce ne.

- Advertisement -

Mann ya sunkuya ya cika gilashin ruwa ya sha a gaban magoya bayansa

Bayan ‘yan kwanaki bayan shan gilashin, Mann ya koka da ciwon ciki mai tsanani

Wani minista dan kasar Indiya wanda ya sha gilashin ruwan datti daga kogin ‘tsarki’ don tabbatar wa mutanen yankin cewa lafiya lau yake ruwam, sai dai daga bisani an kwantar da shi a asibiti bayan ya yi fama da rashin lafiya jim kadan da shan ruwan.

Rahotanni sun ce “Bayan kwana biyu da shan ruwan, Mann ya fara korafin ciwon ciki.”

“An kai shi Asibitin Apollo Indraprastha da ke Sarita Vihar kuma an kwantar da shi cikin dare.”

Likitoci sun ce Mann ya kamu da cuta kuma an tura kwararru sun kula da shi.

Majiyar Muryoyi ta ruwaito cewa, likitoci sunyi gwaje-gwaje iri-iri kan ministan kafin daga bisani aka sallame shi daga asibiti.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: