ASUU ta nemi ayi dokar da zata hana ‘ya’yan jami’an Gwamnati fita karatu a kasashen waje
Daga Muryoyi
Muryoyi ta ruwaito ASUU na cewa “Idan suka yi makaranta a nan kuma ‘ya’yansu suna nan za su nuna goyon baya ga tsarin jami’a da manyan makarantun Najeriya.”
Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi kira da a samar da kudirin doka da zai hana ‘ya’yan jami’an Gwamnati shiga makarantun da ke kasashen wajen.
- Advertisement -
ASUU ta ce “Idan aka yi haka, za a gina al’umma ta gari ta hanyar bunkasa manyan cibiyoyin ilimi da inganta kudade na tsarin jami’a a Najeriya.
“Idan masu hannu da shuni suka je jami’a ko cibiya daya, ba na jin za a sake yajin aiki.
“Idan sun yi makaranta a nan kuma ‘ya’yansu suna nan za su nuna cikakken goyon baya ga tsarin jami’a da kuma manyan makarantun Najeriya,” in ji shugaban Jami’ar Yenegoa.
A ranar 14 ga watan Fabrairu ne malaman jami’o’i mallakin gwamnati suka fara yajin aikin gama gari a fadin kasar, kan kin amincewa da tsarin bayyana gaskiya da rikon amana na jami’ar wato (UTAS) a matsayin tsarin biyan kudi a bangaren jami’ar.
Tun da farko, shugaban kungiyar NLC a Bayelsa John Ndiomu, ya bukaci gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan daftarin yarjejeniyar da aka sake tattaunawa tsakaninta da ASUU.