- Ban zama mataimakin Tinubu don kare musulunci ko musulmi ba –inji Kashim
Daga Muryoyi
Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC kana kuma tsohon Gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima ya tabbatar da cewa Tinubu bai zabe shi mataimakin shugaban Nijeriya domin ya kare addinin musulunci da musulmai ba, shi na kowa ne.
A wata hira da akayi dashi a kafar Talbijin ta turanci, Kashim Shettima ya bayyana cewa sarkin Musulmi shi ke da alhakin kare martabar addinin musulunci da musulmai amma shi domin yin aiki yake takara.
- Advertisement -
Domin aiki yasa muke takara ba domin kariya ga wata kabila ko addini ba, na fada na kara ba Musulunci na fito yiwa aiki ba, hakanan ba wata kabila na fito wakilta ba, Sarkin Musulmi ke da alhakin kare musulunci da musulmai