BIDIYO: ‘Yan ta’adda sunyi wa fasinjojin jirgin kasa bulala sun yi barazanar garkuwa da Buhari da El-Rufai

‘Yan ta’adda sunyi wa fasinjojin jirgin kasa bulala sun yi barazanar garkuwa da Buhari da El-Rufai

Daga Muryoyi

Wata kungiyar ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma ta yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai.

‘Yan ta’addan sun yi wannan barazanar ne a wani sabon faifan bidiyo da suka fitar inda aka gansu suna bulala da danyen itace ga wasu mutanen da suka yi garkuwa da su fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja.

- Advertisement -

Wannan barazanar na zuwa ne makonni kadan bayan harin da aka kaiwa ayarin motocin Buhari a jihar Katsina.

A wani sabon faifan bidiyo, ‘yan ta’addan da suka kai hari a gidan yarin Kuje da ke Abuja kwanan nan suka sako mambobinsu da ke tsare a gidan yari, suna yin barazana ga shugaban kasa da kuma Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna.

‘Yan ta’addan wadanda suka yi garkuwa da fasinjoji sama da 60 na jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, sun kuma yi barazanar kashe wadanda suka rage a hannunsu da kuma takama da cewa za su ruguza kasar.

A cikin faifan bidiyon, daya daga cikin ‘yan ta’addan ya ce matukar gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba, to za su mayar da yankin tamkar wata kwata.

“Wannan shi ne sakonmu ga gwamnatin Najeriya kuma kamar yadda kuka ga wadannan mutane a nan, da yardar Allah za ku ga shugabanninku; Sanatoci da gwamnonin ku za su zo gabanmu.

Wadannan da kuke gani a nan za mu rike wasu a matsayin bayi mu sayar da su kamar yadda Imaminmu ya fada muku a baya,” inji shi.

“Kamar yadda ’yan matan Chibok da aka sayar, za mu sayar da wadannan a matsayin bayi.

“Idan ba ku bi bukatunmu ba, za mu kashe wadanda muke bukata mu kashe mu sayar da sauran. Da yardar Allah, El-Rufai, Buhari, za mu kawo ku nan,” daya daga cikin ‘yan ta’addan ya ci gaba da cewa a cikin harshen Hausa.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: