Buhari ya kira taron gaggawa kan tsaro bayan El-Rufai ya nuna masa bidiyo yan ta’adda na barazanar sace shi

Buhari ya kira taron gaggawa kan tsaro bayan El-Rufai ya nuna masa bidiyo yan ta’adda na barazanar sace shi

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ce yayi wata ganawar gaggawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan tsaro kuma ya sanar dashi bidiyon da yan ta’adda suka fitar suna barazanar sai sun yi garkuwa da shugaban kasar da shi Gwamnan da sauran Gwamnoni da Sanatoci,

El-Rufai a wata hirar kai tsaye da yayi da yan jarida a ranar Laraba, ya ce yan ta’addan sun samu waje ne da har suke da zuciyan ikirarin sace shugaban kasa ko Gwamna a kasar da akwai yan sanda da sojoji.

- Advertisement -

Ya ce har zuwa ranar Lahadi da ya gana da shugaban kasar ya fahimci Buhari bai ma da labarin abunda ke faruwa bai san yan ta’addan sun ce zasu sace shi ba “nan na fada masa abunda ke faruwa tare da wasu yan shawarwarin matakan da ya kamata a dauka akan yan ta’addan” Kodayake daga bisani Gwamna Mutawalle na Zamfara har bidiyon ma ya nunawa shugaban kasar kuma ya kira taron majalisar tsaro domin kawo karshen lamarin.

El-Rufai ya yi bayanin cewa tun shekaru biyar da suka shude ya rika bada shawarar a yi wa yan ta’addan ruwan bama-bamai a duk inda suke, yana mai cewa wannan ne kawai mafita,

Idan dai baku mance ba Shugaban kasar yaki bin wannan shawarar ta kona daji a kashe yan ta’addan a baya saboda gudun kada ya sauka mulki majalisar dinkin duniya ta kama shi da laifin yaki ko take yancin dan Adam kodayake yan Najeriya sun yi zafafan martani akai.

Muryoyi ta ruwaito El-Rufai na cewa kodayake yasan su a matakin su na Gwamnoni suna bakin kokarinsu haka shima shugaban kasar nayin bakin kokarinsa amma dai ya kamata a dauki matakin da ya dace tunda gashi yanzu har yan ta’addan sun fara shiga Abuja.

“Na ma samu labarin bidiyon inda suka yi barazanar sace Buhari da ni. An gargade ni in rika taka tsantsan da iyalai na. Ta yaya za mu zauna
a kasar da yan ta’adda za su rika yi wa Shugaban kasa barazana kuma akwai sojoji da yan sanda?

“Idan a baya wadanda ke gwamnati na ganin abin wasa ne kawai da ke shafar yan Katsina, Zamfara, Kaduna da Niger, to yanzu abun ya shiga Abuja.

“Na gana da shugaban kasa a ranar Lahadi na fada masa matsalolin. Na kuma fada masa batun bidiyon
domin har zuwa ranar bai sani ba. Na fada masa kuma bayan kwana daya gwamnan Zamfara ya sake tabbatar masa kuma shima ya ga bidiyon domin ya dauki mataki”

Gwamnan ya jajantawa wadanda iyalansu ke hannun masu garkuwa kuma ya sha alwashin ana yin kokarin shawo kan lamarin da yardar Ubangiji

“Shugaban kasa ya tabbatar min cewa ya zauna da shugabannin tsaro kwana 3 zuwa 4 kafin haduwar mu kuma ya bawa sojojin umurnin su
magance abin.

Muna fata, da izinin Allah sojoji da
yan sanda da aka bawa umurnin za su gama aikin. Ba sai mun jira yan ta’addan sun kawo hari kafin
mu mayar da martani ba,” in ji El-Rufa’i

Gwamnan na Kaduna ya ce sojojin su bi yan ta’addan duk inda suke su gama da su. Maganan gaskiya shine mun damu da matsalar tsaro kuma
muna fata gwamnatin tarayya za ta dauki matakin da ya dace.

Sai dai ana ganin bayan da shugaban kasar ya kalli abunda ya faru ta sa ya kira taron gaggawa kan majalisar tsaron kasarnan a yau Alhamis

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: