Buhari zai gabatar da lacca kan tsaro a kasar Laberiya

Buhari zai gabatar da lacca kan tsaro a kasar Laberiya

Daga Muryoyi

A ranar Talata ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai tashi daga Abuja zuwa Monrovia, Laberiya, domin yin jawabi da ya shafi tsaro a yammacin Afirka, zabuka na gaskiya da adalci da mutunta doka da sauran su.

Muryoyi ta ruwaito har ila yau, Buhari zai bi sahun sauran shugabannin Afirka taya murnar kasar Laberiya bikin cika shekaru 175 da samun ‘yancin kai; a matsayin kasar Afirka mafi tsufa bayan mulkin mallaka.

- Advertisement -

Fadar shugaban kasar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Litinin mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu mai taken ‘Muhimmancin ziyarar shugaba Buhari a Laberiya.

Ziyarar ta Laberiya na zuwa ne akalla kwanaki biyu bayan fitar da wasu faifan bidiyo da ke nuna ‘yan ta’adda – ciki har da wanda ya tsere daga harin da aka kai gidan yarin Kuje a ranar 5 ga watan Yuli, inda suka yi wa 43 daga cikin fasinjoji sama da 61 bulala wadanda aka yi garkuwa da su daga jirgin kasan Kaduna-Abuja a ranar 28 ga watan Maris.

A cikin faifan bidiyon, ‘yan ta’addan sun yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasar da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Amma Shehu, wanda ya bayyana cewa Buhari na tafiya kasar Laberiya, a ranar Talata, 26 ga watan Yuli, ya ce, “tafiyar na nuna muhimmancin da ke tattare da tsaro da walwalar Laberiya da sauran kasashen yammacin Afirka.”

Sanarwar ta kara da cewa, “A wannan rana, kasar Laberiya ta cika shekaru 175 da samun ‘yancin kai na musamman, inda kasar ta kasance kasa mafi tsufa a Afirka bayan samun ‘yancin kai.

“Shugaba Buhari shine babban bako na musamman a wajen bikin kuma zai gabatar da jawabi. Ziyarar zuwa Laberiya na zuwa ne a daidai lokacin da rashin kwanciyar hankali na siyasa da koma bayan juyin mulkin da aka shafe shekaru biyu zuwa 30 ana yi na dimokuradiyya a yankin.

“Laberiya da Saliyo tare da Najeriya za su yi zabe a 2023 kuma ana sa ran Shugaba Buhari zai jaddada musu mahimmancin zabe na gaskiya mai inganci.”

A nasa jawabin, ana sa ran shugaban ya jaddada muhimmancin mutunta tsarin doka a fadin yankin. Idan babu bin doka da tsarin mulki, ba za a iya samun tsaro da zaman lafiya da ci gaba ba.

A ci gaba da bayar da hujjar tafiyar shugaban kasar, Shehu ya ce “ Zaman lafiya da tsaro na Laberiya (da Saliyo) na da muhimmanci ga Najeriya idan aka yi la’akari da dimbin jari da kayayyaki da kuma albarkatun da kasar nan ta kashe don tabbatar da tsaron jihohin biyu.

“A gefe guda, Najeriya da Laberiya na iya kawo batutuwan da suka shafi ta’addanci a kan iyaka, da karfafa dangantakar tsaro da kasuwanci. Dangantakar da ke tsakanin shugaba Buhari da George Weah na Laberiya nada muhimmanci kuma za ta taka muhimmiyar rawa kan al’amuran gobe.”

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: