Buhari zai raba tallafin Naira dubu 20,000 ga Talakawa miliyan Daya don rage radadin talauci
Daga Muryoyi
Gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin naira dubu ashirin 20,000 ga talakawa da marasa galihu 2,900 a babban birnin tarayya Abuja.
Muryoyi ta ruwaito da take yiwa ‘yan jarida jawabi bayan bikin kaddamar da shirin a Abuja, ministar harkokin jin kai, kula da bala’o’i da ci gaban jama’a, Sadiya Umar Farouq, ta ce manufar shirin shine a taimaka wajen fitar da ‘yan Najeriya miliyan daya daga kangin talauci nan da shekarar 2030.
- Advertisement -
A cewar Ministar an zabo mutane 2,900 da suka ci gajiyar tallafin daga kananan hukumomi shida da ke Abuja.
Sadiya ta ce, “Za a yi ta maimaita makamancin shi a duka sauran jihohin dake tarayyar Najeriya.”
“Mun kaddamar da shirin ne da babban birnin tarayya ayau kuma za mu ci gaba da sauran jihohin nan da mako mai zuwa.
“Wannan shiri ne a karkashin shirin ‘National Social Investment Programme’, wani shiri na shugaban kasa Muhammadu Buhari dake da burin tallafa wa talakawa da marasa galihu da sauran ‘yan kasa yan Najeriya mabukata
“Wannan Naira 20,000 da za a bai wa marasa galihu, tallafi ne na lokaci daya. Kuma an basu ne ko dai a matsayin jari su fara kasuwanci kadan-kadan, ko kuma su kara jari akan wanda suke da shi.” inji ta