Bushewar zuciyar Buhari tayi yawa ai ko Fir’auna sai haka -Sheikh Bello Yabo

Bushewar zuciyar Buhari tayi yawa ai ko Fir’auna sai haka -Sheikh Bello Yabo

Sheikh Bello Yabo, fitaccen malamin addinin Islama dake Sokoto, ya caccaki shugaba Buhari kan halin ko in kula da ya nunawa fasinjojin jirgin kasa dake hannun ‘yan ta’adda.

Malam Yabo yace Buhari ya ci amanar ‘yan Najeriya kuma ya nuna rashin tausayinsa a fili saboda yana da damar ceto jama’a amma ya nuna rashin adalci.

Ya tunatar da shugaban kasan yadda yayi ranstuwa da Qur’ani amma yana nuna rashin tausayi kama Fir’auna, zai bayyana a gaban Ubangji inda bashi da ta cewa.

- Advertisement -

“To wai yaya zaku iya fuskantar Ubangiji da hakkin bayinsa da kuka yi banza da shi? Rantsuwa fa kuka yi. Kai Buhari kana Musulmi aka baka Qurani kayi rantsuwar zaka yi adalci. Yanzu wadannan kayi musu adalci?

“A kama su, kana da yadda zaka iya kwato su amma ka kyale su? Don haka ku ji tsoron Allah, ku tausayawa wadannan bayin Allah. Yanzu ya za ku ji da a ce matanku ne da `ya yanku da yan uwanku aka kama?

Buhari da a ce matar ka ce cikin halin da matan nan ke ciki ya zaka ji? Toh duk yadda za ka ji haka ‘yan uwan wadannan bayin Allah suke ji. Don haka ya kamata ku tausaya musu. Ku ji tsoron Allah, ku sani ba nan za a dawwama ba

 

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: