El-Rufai ya baiwa ma’aikatan Kaduna hutun kwana 3 don su sami damar yin katin zabe

El-Rufai ya baiwa ma’aikatan Kaduna hutun kwana 3 don su sami damar yin katin zabe

Daga Muryoyi

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi kira ga mazauna jihar da su hanzarta zuwa suyi rijistar zabe kafin wa’adin da INEC ta bayar na rufewa a ranar 31 ga Yuli, 2022.

Muryoyi ta ruwaito Gwamnatin jihar ta kuma ayyana ranakun 27 zuwa 29 ga watan Yuli 2022 a matsayin ranar hutu a jihar Kaduna domin ma’aikata su samu damar zuwa su kammala rajistar zaben.

- Advertisement -

El-Rufai ya bukaci daukacin mazauna jihar da su yi amfani da wannan hutu domin yin rijistar zabe, don samun ikon yin amfani da ‘yancinsu na kada kuri’a a ranar zabe.

Kakakin Gwamnan Muyiwa Adekeye ya kuma bayyana cewa gwamnati ta bukaci dukkan ma’aikatu da su tallafa wa ma’aikatansu don yin rajista kafin INEC ta rufe rajistar masu zabe a ranar 31 ga Yuli, 2022.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: