Gwamnatina zata kawo karshen matsalar tsaro –inji Buhari

Gwamnatina zata kawo karshen matsalar tsaro –inji Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari yayi kurarin cewa gwamnatinsa zata kawo karshen matsalar tsaron da kasarnan ke fuskanta, tare da cewa ko kadan bai zai raga wa ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan da ke kai hare-hare a fadin Najeriya ba.

Buhari ya kira ‘yan bindigar a matsayin makiya al’umma wanda a cewarsa ya kadu matuka da kisan da suke yiwa yan Najeriya. Wannan masifa kullum karuwa take yi a kasar nan. Na sani kuna cikin halin damuwa, ina taya ku bakin-ciki

Shugaban kasar ya cigaba da nanata cewa Matsalar tsaro ita ce babban abin da ya sa a gaba, ya kuma umarci manyan hafsoshin tsaron kasar da su yi iya bakin kokarinsu, domin kawo karshen wannan matsala da kasar ke ciki

- Advertisement -

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: