Thursday, March 23, 2023
HomeUncategorizedDuba SuKotu ta tura mai kula da kudaden Najeriya gidan yari bisa zargin...

Kotu ta tura mai kula da kudaden Najeriya gidan yari bisa zargin badakalar N109B

Zargin badaƙalar N109.5b: Kotu ta aike da dakataccen Akanta-Janar gidan yarin Kuje

 

Wata babbar kotun birnin tarayya, Abuja ta bayar da umarnin aike wa da dakataccen Akanta-Janar, Ahmed Idris da wasu mutane uku zuwa gidan yari na Kuje bisa zargin almundahanar Naira biliyan 109.5.

 

Sauran wadanda ake tuhumar sun hada da Olusegun Akindele, Mohammed Usman da Gezawa Commodity Market and Exchange Limited.

 

Hukumar  EFCC ce dai ta gurfanar da su a gaban kuliya, bisa tuhume-tuhume 14 da ake zargi da karkatar da Naira biliyan 109.5.

 

- Advertisement -

Mai shari’a O. Adeyemi Ajayi ta bayar da umarnin ne bayan gabatar da dukkan lauyoyin da ke cikin shari’ar.

 

Ta kuma bada umarnin a ci gaba da tsare waɗanda ake ƙara a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa lokacin da aka neman beli.

 

Ta ɗage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 27 ga watan Yuli domin sauraren roƙon neman beli.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: