Muna duba yiwuwar haramta babura da hakar ma’adinai a fadin Najeriya –FG

Muna duba yiwuwar haramta babura da hakar ma’adinai a fadin Najeriya –FG

 

Daga Muryoyi

 

Kwamitin tsaro ya sanar da cewa, yana duba yiwuwar haramta babura da ayyukan hakar ma’adinai a fadin kasarnan baki daya a wani bangare na dabarun da Gwamnati ke dauka na dakile ayyukan ‘yan ta’adda, da gano matsuguninsu da kuma katse hanyoyin samun kudadensu.

 

Da yake yiwa manema labarai jawabi jim kadan bayan kammala taron da shugaban kasa ya jagoranta kan tsaro, babban Lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike musamman domin tabbatar da alakar da ke tsakanin ma’adanai da babura da suke zargin suna bayar da kudade wajen samar da makamai ga ‘yan ta’adda.

 

 

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito Malami ya kara da cewa ‘yan ta’addan sun kaura daga hanyoyin da suka saba bi wajen samar da kudaden ayyukansu zuwa hakar ma’adinai da karbar kudin fansa, ya bayyana cewa gwamnati tana da masaniya kan illar tattalin arzikin da kudurin da aka tsara zai haifar, musamman dokar hana babura amma ya zama wajibi domin a tabbatar da tsaron kasa.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: