Muna rokon gudunmuwar Malamai da Almajirai kan matsalar tsaro –inji El-Rufai

Muna rokon gudunmuwar Malamai da Almajirai kan matsalar tsaro –inji El-Rufai

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya nuna takaicinsa kan yadda matsalar tsaro ke jawo masu cikas a wajen ayyukan Gwamnati da harkokin bunkasa kasa da zuba jari,

A cewar Gwamnan kodayake dai Gwamnatin Muhammadu Buhari tana yin bakin kokarin ta kan tsaro to amma ya kamata a kara hobbasa domin ganin an kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya,

- Advertisement -

“tun shekara Biyar da suka wuce nake bayar da shawarar a bi yan bindigar nan har mabuyarsu ayi masu ruwan wuta ta sama da kasa duk a kashe su, masu tunanin cewa Kaduna da Katsina abun ke faruwa to yau gashi ya zo Abuja don haka dole a tashi tsaye ”

Muryoyi ta ruwaito Gwamnan na cewa a yayin da Gwamnati ke nata bakin kokarin ta suna kuma rokon Malaman addini da almajirai a dage da rokon Allah ya baiwa Gwamnati da jami’an tsaro sa’a akan miyagun.

“Muna kira ga al’umma da malamai da almajirai da limamai da fastoci ayi ta mana addu’oi ayi ta yi ma jami’an mu addu’oin Allah ya kare su Allah ya kara karfafa zuciyarsu suyi yakin wannan abun” inji El-Rufai

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: