Naji kamar an soka mani mashi lokacin da aka sanar da ni an kashe Deborah –inji mahaifiyarta 

Sai da naji kamar an soka mani mashi lokacin da aka sanar da ni an kashe Deborah –inji mahaifiyarta

 

Daga Muryoyi

 

Duk da tsawon lokaci da aka dauka da faruwar lamarin, Alheri Emmanuel, mahaifiyar matashiyar nan daliba Deborah Samuel – wacce aka kashe a Jihar Sokoto bisa zargin batanci ga Annabi S.A.W – mahaifiyarta ta ce ta ji kamar an soka mata mashi lokacin da ta samu labarin kisan ‘yar tata.

 

 

A wata tattaunawa da tayi da BBC Alheri wacce ke bayani cikin kuka da tsananin tashin hankali ta ce, an kira ta a waya lokacinda abun ke kan faruwa.

 

- Advertisement -

Daliba

Batanci ga Annabi S.A.W shine masifa da bala’i da tashin hankali mafi kololuwa ga musulmi kuma malaman addinin Musulunci sun jaddada cewa “duk wanda aka tabbatar ya yi ɓatanci ga Annabi hukuncinsa kisa ne”, to amma malaman sun ce ba mutanen gari ne za su zartar da hukuncin ba kodayake wasu na ganin hukumomin ne basa yin abunda ya kamata idan an kai karar wani yayi sabo.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: