“Ruwan sama yaki daukewa gashi gawayina ya jike, gashi an rushe rumfar Mai shayin” –Gwauraye sun bayyana yadda suke jin jiki a Kaduna 

“Ruwan sama yaki daukewa gashi gawayina ya jike, gashi an rushe rumfar Mai shayin” –Gwauraye sun bayyana yadda suke jin jiki a Kaduna

Daga Muryoyi

Gwauraye da Tazurai na dandana kudarsu a Kaduna bayan sabbin gyare-gyare da akayi a jihar wanda yasa a yanzu ba kasafai masu shayi da sayar da abinci ke bude wajajen kasuwanci ba

Gwamnatin jihar Kaduna a shirin da tayi na tsara birnin Kaduna tayi wasu rushe-rushe da fadada hanyoyi da yin wasu domin kawata jihar kodayake hakan ya zo da nashi azabtarwar ga wadanda suka dogara da masu shayi da abincin sayarwa

- Advertisement -

“Tashin hankali ruwan sama yaki daukewa gashi gawayi (charcoal) din ya jike, gashi an rushe rumfar Mai shayin” wani gwauro mai suna Kwamared Zaharadeen ya rubuta a shafinsa na Facebook wanda ya jawo ake ta muhawara

Ya kuke ji da rayuwa a matsayin ku na gwauraye musamman a wannan lokaci na damina?

Ku bayyana mana a comment…

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: