Tsabar son Aure ta sa wani matashi hada hotonsa da wata budurwa don ace masa Ango

Tsabar son Aure ta sa wani matashi hada hotonsa da wata budurwa don ace masa Ango

Daga Muryoyi

Saboda bala’in son Aure wani matashi yayi “editing” ya hada hotonsa da wata budurwa domin a ce masa Ango.

Sai dai Muryoyi ta ruwaito kakar matashin ta yanke saka domin kuwa Budurwar mai suna Zainab Ishaq ta ga wannan hoto kuma yayi mata dadi har ma tayi martanin cewa tayi na’am da wannan matashi kuma ya zo su sasanta idan ya shirya suyi auren gaske “kodayake sai anyi bincike akansa tukunna”

- Advertisement -

Zainab ta ce “Ni da naga ana ta mentioning di na, yaseen ban je na duba ba ma, sai da naga ana ta aiko min ta inbox, yesss hoto na ne, kuma gidan jaridu ga sako, ku fadawa wancen matashi, idan har ya shirya, ya zo ni ma na shirya, amma akwai interview!!!!!”

Yanzu wace shawara zaku bawa wannan matashi?

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: