Turai zata hada hannu da Buhari domin maye gurbin Gas din Rasha da na Najeriya

Turai zata hada hannu da Buhari domin maye gurbin Gas din Rasha da na Najeriya

Daga Muryoyi

Tawagar Tarayyar Turai EU da ECOWAS ta ziyarci Najeriya domin tattauna yadda za ta maye gurbin iskar gas din da take saye daga kasar Rasha zuwa iskar gas na Najeriya sakamakon mamayar da Rasha take yi a kasar Ukraine.

Bayanin hakan ya fito ne daga Mataimakin Darakta-Janar na Sashen Makamashi a Hukumar Tarayyar Turai a Brussels, Mista Matthew Baldwin, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai jiya Juma’a a Abuja.

- Advertisement -

Majiyar Muryoyi ta ruwaito cewa Baldwin zai gana da manyan jami’an gwamnatin Najeriya da ‘yan kasuwa masu zaman kansu, ciki har da masu ruwa da tsaki a bangaren makamashi na kasar.

NAN ta ruwaito cewa kungiyar zartaswa ta EU ta bukaci kasashe mambobin kungiyar da su rage yawan iskar gas da suke amfani da shi da kashi 15 cikin 100 yayin da ta yi gargadin cewa “da yuwuwar rufe halaka ko sayen kayayyakin Rasha gaba daya”.

Tun bayan mamayar Ukraine ne da Rasha tayi, kungiyar tarayyar Turai wato EU take ta kokarin kawar da huldar kasuwanci da sanya takunkumi ga Rasha

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: