Wadanda kuka ce zaku kama Allah ya baku sa’a ku kamo su amma ku sako wadanda ke hannun ku –Bello Yabo
Daga Muryoyi
Fitaccen malamin addinin nan na garin Sokoto, Malam Bello Yabo ya saki wani bidiyo da ya jawo cece-kuce inda a ciki aka hango shi yana cewa:
“Muna yi masu addu’a masu kamen Allah ya baku sa’a yaku masu kame ku matsa zamu taimaka maku da addu’a Allah ya baku sa’a ku kamo shi ”
- Advertisement -
Muryoyi ta ruwaito a bidiyon Sheikh Bello Yabo ya cigaba da cewa “Wadannan da kuka ce zaku kama Allah ya baku sa’a ku kamo su amma ku sako wadancen wadanda ke hannun ku. Inda irinsu ne ma kuke kamawa ai da ba ruwanmu, mu wallahi da albarka ma zamu saka maku don sun zaman mana bala’i”
“Meye amfaninsu. Sun gaza, Inda su ne ma kuka kama kukayi cikin daji kuna yi masu sanduna”
“Amma bayin Allah basu san hawa ba basu san sauka ba kila ma wani wajen neman abinci zashi kun kama shi baku barshi da bakin cikin da yake ciki ba kuma kun kama bugunai to ya zakuyi da hakkinsu?”
“Don haka ku kama wadancen, kuyi niyya ku kama shi, mu ka rokawa, bamu rokan mai ko kuna roko a sako shi? Wallahi nidai bani roko in aka kama shi. Ni wallahi dadi zan ji sai na zuba ruwa ga kasa na sha in aka kama shi kuma Allah kasa a kama shi” inji Bello Yabo