‘Yan ta’adda na hada makamai domin kai kazamin hari mahaifar Buhari – NSCDC

‘Yan ta’adda na hada makamai domin kai kazamin hari mahaifar Buhari – NSCDC

Daga Muryoyi

Jami’an tsaron NSCDC sun banakado wani shiri da yan bindiga ke yi na kai hari maihaifar shugaban kasa, Muhammadu Buhari wato jihar Katsina, da Kaduna, da kuma Legas, da babban birnin tarayya, da dai sauransu.

Hukumar NSCDC ta bayyana cewa ta samu bayanan sirri cewa, ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP, sun tattara mayakansu sun basu horo tare da samar masu da muggan makamai kamar na’urorin kakkabo jiragen sama, manyan bindigogin yaki, da dai sauransu, a shirye-shiryen kai kazaman hare-haren a jihar da shugaban kasar ya fito.

- Advertisement -

Majiyar Muryoyi ta ruwaito hukumar tsaron na cewa, “Mun samu sahihin bayanan sirri cewa Boko-Haram da kungiyoyin ta’addancin ISWAP sun hada mayaka da manyan muggan makamai musamman masu harba rokoki, bindigogin kakkabo jiragen sama, da manyan bindigogin Janaral Purpose Machine da su ka yi niyyar turawa domin kai farmakin. a jihar Katsina.”

Rahoton ya kuma yi ishara da wasu hare-haren da kungiyoyin ‘yan bindiga ke shirya kaiwa a jihohin Legas, da Abuja Babban Birnin Tarayya, da Kaduna, da kuma Zamfara.

A don haka aka umurci kwamandojin jihohin da su sanya ido sosai su dauki matakin dakile hare-haren.

“A wani labarin kuma, an bankado kungiyoyin ‘yan bindiga guda biyu na shirin kai hare-hare tare na hadin gwiwa a yankin Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da kuma Kudu maso Yamma (Katsina, Zamfara, Kaduna, Kogi, FCT da Legas).

“Saboda haka, Babban Kwamandan ya umarce ku da ku tabbatar da tsaurara tsaro a duk wurare masu mahimmanci da suka hada da Makarantu, Cibiyoyin Ibada, da Muhimman kadarorin kasa a jihohin ku, don bincikar duk wata barazanar da wadannan masu aikata laifuka ke yi ”in ji wani rahoton Umurni da NSDC ta aikewa kwamandojin ta.

Majiyar Muryoyi ta PUNCH ta tuntubi kakakin hukumar NSDC, Shola Odumosu domin jin ta bakinsa akan lamarin amma har ya zuwa lokaci hada wannan rahoto bai samu ba yin karin bayani akai ba.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: