YANZU-YANZU: Rikici ya barke a zauren majalisa bayan wasu Sanatoci sunyi yunkurin tsige Buhari
Daga Muryoyi
A yau Laraba ne Sanatoci daga jam’iyyun adawa suka fice daga zauren majalisa domin nuna fushinsu kan kunnen uwar shegu da kakakin majalisar yayi bisa kudurin da aka gabatar na a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Muryoyi ta ruwaito Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Phillip Aduda, ne ya gabatar da wani batu inda ya bukaci shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya tattauna batun tsaro da kasar ke fama da kuma batun tsige shugaba Buhari bisa gazawarsa.
- Advertisement -
Sai dai majiyar Muryoyi ta ruwaito Sanata Lawan, wanda ya jagoranci zaman majalisar a yau ya ki amincewa da bukatar shugaban marasa rinjaye, yana mai cewa batun bashi da tushe bare makama.