Thursday, March 23, 2023
HomeUncategorizedDuba SuABUNDA YA FARU: Budurwa ta sha fiya-fiya ta mutu a Zaria

ABUNDA YA FARU: Budurwa ta sha fiya-fiya ta mutu a Zaria

ABUNDA YA FARU: Budurwa ta sha fiya-fiya ta mutu a garin Zaria

“A ranar alhamis data gabata (28/07/22) , aka fahimci akwai wani makwabcin marigayiyan wato Mai Suna Nana, Wanda yake aiki a cibiyar makarantar horas da Malamai na FCE Zariya, Yana bibiyan ita marigayiyan da Suna fasikanci.

Al’amarin Sanan Nan abune, Wanda kowa a wannan anguwar na Anguwar Alkali Zariya yasan halin shi Wai Shi (Dan Zaki), na lalata yara mata ta inda duk Wanda aka ganshi da ita akan yi mata zargi.

Daganan sai yan uwan Mahaifin marigayiyan suka kirata suka karba wayan hannunta Wanda Nokia ce da Bata wuce 4,000 ba, suna danna number wannan mutumin sai sukaga sunanshi ya fito daganan sai suka ajiye wayar har sai sunyi bincike sanan su kirata suja mata kunni akan ta Kare mutuncin kanta dana gidansu.

- Advertisement -

Bugu da Kari, kafin a kaiga wannan lokacin sai kawai akaji labarin Wai tasha fiya fiya sabida Wai ita a cewarta an tsaneta sabida mene yasa ita kadai a ka karbi wayarta ba’a karbi na sauran yaran gida ba.

Daganan sai ta dauki fiya fiyar tasha dan kadan Wai ita a wautarta zaidan jikata ta ko a tausaya mata amma abin sai yazo da karar kwana, domin alokacin tagaya wa wacce take rukonta cewa tasha Amma ita kuma bata dauki matakiba har saida wata bakuwa ta shigo take tambaya mene ya faru da wance (marigayiyan Nana) sai ita Mai goyon nata take fada mata Wai fiya fiya tasha, daga nanne fa ita bakuwan tanemi agaji amma alokacin fiya fiyan ya dade a jikin marigayiyan kafin a kaita asibiti rai yayi halinshi.

Shi Kuma wannan azzalumin Mai yawan jimirin lalata Yara, Sai yayi amfani da wannan damar na cewa ai akan Saurayi ne Tasha fifiya ta mutu, don kada Aisirnsa ya tuno.

Dangane da Al’amarin shi Kuma Saurayin nata, majiyarmu ya tabbatar Mana cewa, tabbas marigayiyar tana da Saurayin da Suka shaku na matukar gaske Wanda daga Karshe Suka rabu.

Rabuwar marigayiyar da Saurayinnata, bashi da alakar Shan fiya fiya, bisani an tabbatar Mana cewa, tsakanin ita da Saurayinnata Sun je aka Yi masu gwajin jini a domin tabbatar da jinsin kowanne nau’in jini a tsakaninsu.

Majiyarmu ya Kara tabbatarwa da Alfijir Hausa cewa, tun a wurin gwajin jini aka Samu matsala, na da yuwuwar idan Sukayi aure zasu haifi Mai cutar Sikila, a nan kowa ya cire Rai da kowa aka rabu aka koma mutunci, Amma Shan fiyafiyar marigayiyar wato Nana da har ya yi Sanadiyar halakata Sam bashi da alaka da rabuwarta da Saurayinta.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: