Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuHanyar samun kuɗi ta kan gabatar da ayyuka a fannoni daban daban...

Hanyar samun kuɗi ta kan gabatar da ayyuka a fannoni daban daban ta yanar gizo (1)

Hanyar samun kuɗi ta kan gabatar da ayyuka a fannoni daban daban ta yanar gizo (1)

Rubutawa; Aliyu Samba

A wannan rubutu na farko zan fara ne da fitowa da masu saƙafa a fannoni guda biyar wasu hanyoyi da zasu samu kuɗin da baza su gaza ₦100,000 ba a wata.

Masu kwarewa a ɓangaren IT Development wato saƙafar ƙirƙira da fasaha, masu kwarewa wajen iya design na Graphics, kwararru a fannin kasuwanci, kwararru wajen iya rubutu, fassara daga turanci zuwa wasu yaruka, da kuma transcribing, ma’ana juya magana ta video ko audio zuwa rubutu.

- Advertisement -

Ga duk wanda yake da baiwa a ɗayan waɗannan fannoni zai shiga shafin www.upwork.com sai yayi register. Zasu bukaci ka bude profile da zai ƙunshi bayanan ka gaba ɗaya da wuraren da kake da kwarewa, wanda hakan zai saukaka musu wajen yi masa jerin gwanon ayyukan dake da alaƙa da fannin da kake da kwarewa, ko kuma kayi searching a wajen da ke da alamar search da abinda kake da kwarewa akai.

Misali sai ya zama abinda kake son yi shine fassara daga turanci zuwa Hausa, sai ka rubuta (Translation) a wajen search ko ka rubuta (Translation English to Hausa) ko wani yare da kake da kwarewa a kai, zaka samu jerin kamfanonin da suka ajiye ayyukan da suke buƙatar ayi musu na fassara.

Kowanne aiki zaku ga farashin sa a gefe a lissafin Dollar. Sai ku duba ku zaɓa sannan ku nema cewa zakuyi a inda aka sa ”Apply”. Idan suka yarda kayi zasu biya ka ne kafin ko bayan ka kammala, ya danganta da tsarin wannan kamfani ko ma’aikata. Haka idan Transcribing zakayi, ko kuma Graphics design da sauransu kamar yadda na ambata a sama.

Duk wanda yake bukatar ƙarin haske zai samu a kan shafin nasu, ba sai Aliyu Samba yayi bayanin komai da komai daya bayan daya ba. Wannan da nayi ina da kyakkyawan zaton ya share fage wa mutane da dama su fahimta su kuma ribata.

A makon da ya wuce akwai waɗanda na turawa sukai wani aikin transcribing na video mai Mintuna 10, kowannen su ya samu Dalar Amurka 100, wanda darajar sa zai kai kimanin ₦60,000. Sun kuma kammala cikin kwana 2.

Cike duk bayanan da ake bukata a profile din zai taimaka wajen samun aikin fiye da wadanda basu cike ba. Kuma da yawan mutanen mu na arewa basu san wannan tsarin ba, takwarorin mu na kudu sun fi mu amfana daga ire iren waɗannan ayyukan. A yaɗa dan wasu ma su amfana.

©Aliyu Samba
10/8/22

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: