INDA RANKA: Wani mutum ya sanya wa dansa suna ABCDEF GHIJK kuma ya fadi dalilinsa

Wani mutum ya sanya wa dansa suna ABCDEF GHIJK kuma ya fadi dalilinsa

Yaro dan shekara 12 daga Indonesia ya shiga kanun labaran duniya saboda sunan sa mai ban mamaki na ABCDEF GHIJK

Kwarai kuwa daidai ka karanta sunan. Wani ne ya rada ma dan sa sunan haruffa 11 na farko daga haruffan turancin ingilishi. Wannan suna mai ban ta’ajibi ya bayyana ne lokacin da yaron mai shekara 12 ya je allurar rigakafi da yan sandan yankin su suka kaddamar.

Da fari ma’aikatan lafiyar sun dauka cewa yaron wasa yake har sai da suka ga sunan shi ABCDEF GHIJK rubuce a katin shaidar haihuwarsa. Ai nan da nan kuwa hoton takardun yaron, katin shaidar sa da kuma rigarsa wadda sunan sa ke rubuce a jikinta suka karade kafofin sadarwar zamani lungu da sako sati guda bayan yan sanda sun watsa hotunan.

- Advertisement -

Kamar yadda aka ruwaito da fari a makarantar karamar sakandiren da yaron yake karatu ya zama abin dariya. Duk inda ya shiga sai ayi tayi masa dariya, shi kuma yana nokewa. Amma a hankali sai abun ya koma abin alfahari ga yaron. Ana kiran sa da ADEF saboda ya fi saukin fada da kuma saukin rikewa.

Mahaifin yaron, Zulfahmi, ya shaida wa yan jarida cewa yayi niyyar sanya sunan shekara shidda kafin a haifi yaron, ya kara da cewa shi masoyin wasan harhada kalmomi ne daga haruffa, kuma yana matukar kaunar ya zama marubuci.

Wannan ya sanya masa bala`in kaunar harrufan turancin ingilishi ta yadda yanzu haka yana da niyyar sanya ma dan sa na biyu sunan NOPQ RSTUV sannan na ukkun ya sanya mashi XYZ

Matar Zulfahmi bata amince da wannan niyya ta mijinta ba na sanya ma `ya`yan ta sunan wani bangare na haruffan turanci. Shi yasa ma’auratan suka sanya wa kannen ABCDEF GHIJK sunan Ammar da Attur.

Shi dai wannan yaro dan shekara sha biyu cikakken sunan sa shine ABCDEF GHIJK ZUZU, inda zuzu ya samo asali daga haruffan biyun farko na sunan mahaifin shi da kuma mahaifiyarsa watau Zulfahmi da kuma Zuhro.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: