KANO TA LALACE: Allah ya bamu Gwamna mai zuciyar El-Rufai ya gyara mana Kano –Bashir Ahmad

KANO TA LALACE: Allah ya bamu Gwamna mai zuciyar El-Rufai ya gyara mana Kano –Bashir Ahmad

Daga Muryoyi

Hadimin Shugaban kasa kan sadarwa, Bashir Ahmad ya koka game da rashin kyawun tituna a birni da kauyakun Kano yana mai fatan Allah ya kawo Gwamna mai zuciya irin na El-Rufai domin gyara jihar kamar yadda Malam Nasir yayi a Kaduna.

Bashir a shafinsa na Facebook ya rubuta ‘Fatan sabon Gwamnan Kano da zai zo a 2023 zai fi maida hankali wurin gyara da giggina sababbin hanyoyin cikin birnin Kano da kewayen ta, musamman tunda tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso yayi kokari da tunani wurin samar da gadoji sama dana kasa, wanda Gwamna Abdullahi Ganduje shi ma ya dora a kai.

- Advertisement -

Duk da birnin Kano yana da taswirar hanyoyin shige da fice, amma kusan dukkan wadannan hanyoyi a yanzu suna cikin mummunan yanayi musamman a irin wannan lokaci na damuna, da dama irin wadannan hanyoyin ko biyuwa ba sa yi idan an yi ruwan sama.

Muna fatan sabon Gwamnan da zai zo zai yi amfani da dabaru da tsare – tsare irin na Gwamna Nasir el-Rufai na jihar Kaduna wajen sabunta birnin Kano ta yadda zai tafi kafada da kafada da birane na zamani wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Kano da samarwa miliyoyin jama’a ayyukan yi.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: