Thursday, March 23, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMuna samun gagarumar nasara a yaki da ‘Yan ta'adda – Buhari ya...

Muna samun gagarumar nasara a yaki da ‘Yan ta’adda – Buhari ya fadawa Jami’an Diflomasiyya

Muna samun gagarumar nasara a yaki da ‘Yan ta’adda – Buhari ya fadawa Jami’an Diflomasiyya

Daga Muryoyi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Gwamnatin Najeriya na kokarin shawo kan matsalar ‘yan fashi da ta’addanci da sauran miyagun ayyuka a kasar.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da yake karbar wasikun soma aiki daga sabbin manyan kwamishinan kasar Canada a Najeriya Ambasada James Kingston Christoff da jakadan kasar Mexico a Najeriya Juan Alfred Miranda Oritz a fadar gwamnati dake Abuja.

- Advertisement -

Majiyar Muryoyi ta ruwaito Buhari a ya kuma yi kira da a kara hada kai a kasashen duniya domin magance matsalar rashin tsaro, sannan ya bayyana cewa Najeriya ta samu ci gaba mai ma’ana wajen magance matsalar rashin tsaro tare da tallafin kasashen waje da suka hada da Canada da Mexico.

Sai dai yaji takaicin cewa “Rikicin siyasa a Libya na ci gaba da rura wutar ta’addanci a yankunan Sahel, Yamma da Afirka ta Tsakiya,” in ji Buhari.

“Ba a bar Najeriya a baya ba yayin da muke fafutukar kawar da kasarmu daga ‘yan fashi, masu garkuwa da mutane, rikicin makiyaya/Manoma da tada kayar baya. Duk da haka muna samun ci gaba mai ma’ana tare da goyon bayan kasashe waje irin ku don ci gaba da wannan yaki har sai mun shawo kan wadannan kalubale.”

Babban kwamandan ya koka kan yakin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa ya kawo cikas ga kokarin da ake yi na inganta samar da abinci a duniya.

Ya kuma yi imanin cewa rashin tsaro a duniya da kuma annobar COVID-19 da ta addabi duniya a shekarar 2020 ta shafi manyan kasashe masu karfin tattalin arziki.

A wajen taron na daukar sabbin jakadun, shugaba Buhari ya horesu su dora kan nasarorin da magabatansu suka tsaya, yana mai jaddada cewa Najeriya tana kara dogaro da goyon bayansu musamman wajen magance matsalolin da suka shafi teku da sauransu.

A game da babban zaben shekarar 2023, shugaban kasar ya bukaci jami’an diflomasiyya da su sanya ido a kan harkokin siyasa a kasar amma kada su nuna bangaranci a siyasar.

Ya kara da cewa, “Al’ummai suna ci gaba da kokawa don murmurewa daga waɗannan ƙalubalen duniya. Yakin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine ya kawo cikas ga ci gaban da kasashen suka samu wajen magance matsalar abinci a cikin shekaru goma da suka gabata.” Inji Shugaban kasa Muhammadu Buhari

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: