Sheikh Bello Yabo yayi addu’ar Allah yasa a sace Buhari, El-Rufai da Garba Shehu

Sheikh Bello Yabo yayi addu’ar Allah yasa a sace Buhari, El-Rufai da Garba Shehu

Shahararren malamin addinin musuluncin nan dake garin Sokoto, Bello Yabo, yayi addu’ar Allah ya sa masu garkuwa su samu nasarar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, da Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu kamar yadda ‘yan ta’adda suka yi ikirarin garkuwa da su a wani bidiyo.

Idan dai za a iya tunawa, ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjoji a cikin jirgin kasa zuwa Kaduna, sun fitar da wani faifan bidiyo a makon da ya gabata, inda suke nuna yadda suke azabtar da fasinjojin da suke rike da su tare da yin barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, Gwamnan jihar Kaduna, da wasu ‘yan majalisar dokokin kasar idan ba su bi bukatunsu ba.

Da yake mayar da martani ga faifan bidiyon, mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce, “aikin ta’addanci ta amfani da farfaganda da kuma amfani da tashin hankali wajen tilastawa gwamnatoci karba ko mika wuya ga bukatun siyasa ba sabon abu bane a duniya.”

- Advertisement -

Sai dai majiyar Muryoyi ta ruwaito da yake mayar da martani ga kalaman Mista Shehu, malamin ya caccaki mai magana da yawun shugaban kasar saboda bayyana bidiyon a matsayin shiri (farfaganda).

Daily Nigeria ta ruwaito Malamin ya zargi Mista Shehu da cewa bai damu da halin da masu garkuwa da mutane ke ciki ba, ya kuma yi addu’a Allah yasa Garba Shehu ya fada hannun masu garkuwa da mutane.

“Ina rokon Allah yasa su sace ka, Garba Shehu, kuma su yi maka yadda sukayiwa fasinjojin tunda ka ce farfaganda ce,” in ji Mista Yabo.

Sheikh Bello Yabo ya kuma yi kira ga ‘yan ta’addan da su saki wadanda ba su ji ba ba su gani ba dake hannunsu, malamin ya yi fatan Allah yasa ‘yan ta’addan su samu nasara a cikin barazanar da suke yi na sace duk wadanda suka yi barazanar sacewa.

“Muna yi muku addu’a masu garkuwa da mutane. Allah Ya ba ku nasara wajen aiwatar da barazanar da kuke yi na sace wadannan mutane. Amma don Allah a saki mutanen da ba su ji ba ba su gani ba dake rike a hannun ku.

“Idan da irin wadannan mutane ne zaku yi garkuwa da su, da ba mu dami kanmu ba. A maimakon haka, da addu’a da kuma albarka zamu saka maku domin sun zama bala’i [a gare mu].

“Waɗannan mutane ne waɗanda suka yi alkawarin sama da ƙasa, kuma yanzu sun sami dama amma sun kasa cikawa. Ku kai su daji ku yi musu bulala, maimakon a wulakanta ’yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba, masu fafutukar ganin sun biya bukatunsu.

“Kuma don Allah ku matsa da barazanarku, kuma za mu tallafa muku da addu’a Allah ya baku sa’a ku kama shi,” in ji Malam Yabo a cikin harshen Hausa.

Shehin Malamin wanda ke magana a fusace ya ce shi mai goyon bayan shugaban ne kafin ya zama mai adawa saboda gazawar Gwamnati.

 

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: