Wani mutum yayi wa matar abokinsa fyade mijin na gefe yana sharbar bacci

Wani mutum yayi wa matar abokinsa fyade mijin na gefe yana sharbar bacci

Daga Taskar Labarai

Rundunar yan sanda a Lagos ta kama wani magidanci dan shekara 39 bisa zargin yiwa matar abokinsa fyade har gida a lokacinda mijinta ke bacci,

Taskar Labarai ta ruwaito mutumin ya balla gidan abokin nasa a garin Surelere ya shiga suna bacci ya afkawa matar abokin nasa yayi ta saduwa da ita,

- Advertisement -

Sai dai a cewar matar da farko ta zaci mijinta ne amma daga bisani da saduwar ta yi yawa ta mike hannuwa sai ta ji alamar mijinta a gefenta yana barci lamarin da ya jawo tayi ihu har mijin nata ya farka ya kunna wuta sai kwatsam suka ga abokinsa akanta turmi cikin tabarya, lamarin da ya tada kura.

Sai dai kwarton yayi ikirarin cewa ba a cikin hayyacinsa ya aikata abunda ya aikata ba. Ya fasa gidan ya shiga har ya sadu da matar ya ce “ya shawu yayi mankas ne yayi batan hanya”

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: