Thursday, February 2, 2023
HomeAddini da RayuwaAbubuwa Hudu da kowace mace bata so  --inji Malam Daurawa

Abubuwa Hudu da kowace mace bata so  –inji Malam Daurawa

Daga shafin Muryoyi

1. Mace bata son tayi kwalliya ka kushe, akwai auren da na kasa gyara shi saboda mijinta ya kushe mata kwalliya.

2. Kada kace mata tsohuwa, ko kun shekara 60 da mace kada kace mata tsohuwa, sun fi so ka rika yi masu kirari kana ce masu “kina nan a yadda kike bakya tsufa”

3. Kada tayi girki kace baiyi dadi ba, ko Annabi S.A.W bai taba yi ba idan an kawo abincinda bai yi masa ba sai yayi shiru idan ba zai ci ba sai yayi shiru!

- Advertisement -

Idan anyi mistake gishiri bai ji ba, ko gishiri yayi yawa ko mai bai ji ba ko mai yayi yawa ko dandanon bai yi dadi ba kada ka kushe gwara kayi shiru ka ki ci din. Kushe abincin yana yiwa mace ciwo a zuciyar ta.

4. Kada ka yabi wata a gabanta, duk yadda mace take son ka kada ka kuskura ka yabi wata mace a gabanta, ko wacece,

Wannan ya hada da ko a cikin matan ka ne, kada ka rika yabon dayar a wajen sauran matan, wannan abun yana ci masu rai. Mace tana da kishi zuciyarta tana tafarfasa idan ka yabi wata mace a gabanta… kai wataran idan ka samu mai kishi ko mahaifiyar ka ka yaba sai ta ji haushi… Mace bata son haka don haka ya zama Dole sai ka iya siyasa ta tafiyar da iyali.

Wadannan sune abubuwan guda Hudu da kowace mace bata so ko budurwa ko matar aure kamar yadda Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya zayyano.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: