Thursday, February 2, 2023
HomeKasashen WajeAn kafa dokar hana karin Aure da haihuwar ya'ya barkatai a kasar...

An kafa dokar hana karin Aure da haihuwar ya’ya barkatai a kasar Nijar

An kafa dokar hana karin Aure da haihuwar ya’ya barkatai a kasar Nijar

Daga Muryoyi

Shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum ya kafa dokar hana karin aure kan ministocinsa da duk wani mai mukamin Gwamnati a fadin kasar,

Muryoyi ta ruwaito Shugaba Bazoum ya ce daukar wannan mataki na kayyade iyali ya zama dole ne duba da yadda kasar Nijar ke kara durkushewa ta fannin cigaba da tattalin arziki a sakamakon yawan haihuwar ‘yaya barkatai.

- Advertisement -

Ya ce Bankin duniya ya ayyana Jamhuriyar Nijar a matsayin daya daga cikin kasashen Afrika ta Yamma masu fama da matsanancin talauci,

Ya ce ko kasashen Larabawa da ake koyi dasu wajen addini basa haihuwar ya’ya barkatai, basa wuce ya’ya 2 ko 3 amma abun takaici sai ka ga magidanci a Nijar ya haifi ya’ya 10, ko 20 ko 30

“Don haka na bayar da umurni kada wani minista ko mai rike da mukamin Gwamnati ya kara aure, idan mutum na sha’awar kara aure to ya ajiye mukaminsa” inji shugaba Bazoum

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: