Diyar Ganduje ta maka mijinta Kotu a raba Aurensu
Daga Muryoyi
Wata kotun Shariah a Kano ta baiwa maigidan diyar Ganduje mako Biyu ya sasanta da mai dakinsa Asiya-Balaraba ko kuma a raba Aurensu
Majiyar Muryoyi ta ruwaito Asiya-Balaraba Ganduje ta shigar da kara gaban kotun shari’a tana neman a raba auren ta da mijinta Inuwa Uba bisa wasu dalilai.
- Advertisement -
Sai dai Alkalin kotun Khadi Abdullahi Halliru ya baiwa maigidan nata mako biyu ya rarrashi matarsa sannan ya dage karar zuwa ranar 5 ga watan Janairu 2023 domin yanke hukunci.
Majiyar Muryoyi ta ruwaito shekarar su 16 da aure, kuma mijin nata ya roki kotu kada ta raba auren domin yana son matarsa