Gwamnonin Najeriya zasu gana da Buhari domin tursasa shi ya hana CBN aiwatar da sabon tsarin cire kudi
Daga Muryoyi
Gwamnonin Najeriya sun hada kai zasu gana da Buhari domin a hana babban bankin Najeriya CBN aiwatar da sabon shirinsa na takaita cire kudi a Banki
Gwamnonin sun ce kayyade cire kudi zuwa dubu 20 a kullum ko dubu 100 a sati zai kassara tattalin arzikin Najeriya kuma zai fi shafar mazauna karkara wadanda galibinsu basa amfani da banki
- Advertisement -
Bugu da kari kuma wannan shiri zai jawowa shugaba Buhari bakin jini a wajen talakawa
Muryoyi ta ruwaito Gwamnonin suna so shugaba Buhari ya dakatar da wannan tsari na Gwamnan CBN