Thursday, February 2, 2023
HomeLabaran DuniyaYa'ya sun tsinewa gawar mahaifinsu saboda ya mutu bai bar masu komi...

Ya’ya sun tsinewa gawar mahaifinsu saboda ya mutu bai bar masu komi ba

Ya’ya sun tsinewa gawar mahaifinsu da ya mutu bai bar masu komi ba

Daga Muryoyi

‘Ya’yan wani dan Najeriya da ya rasu yana da shekaru 66 a duniya sun tada kura bayan da suka rubuta mummunar shaida kan mahaifin nasu a wajen jana’izarsa

Muryoyi ta ruwaito a cikin tarihin rayuwar mutumin da ya bazu a intanet, yaran mutumin mai suna Gabriel Osanwa sun ce ko da yake dan adam tara yake bai cika 10 ba amma mahaifinsu bishiyar giginya ne, “bai bar mana gadon komi ba”

- Advertisement -

Yaran sun caccaki marigayin da cewa yana kyautatawa mutanen waje yayin da ba ya kula da gidansa (iyalansa).

Kalli hoton takardar ta’aziyyar

“…Hakika ka kasance mai kyautatawa ga mutanen waje amma ka bar gidanka cikin talauci da wahala, A matsayinmu na ya’yan ka, munyi nadamar samun ka a matsayin uba, kodayake duk ketar ka yau ga ka a gabanmu zamu turbude ka a cikin kasa, zamu bar ka kaida halin ka”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: